<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Edward Mote, Hillsong</author>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Yesu, kayan adona
 Jininka ne da giciyenka.
 Ko duniya dai ta yi gobara,
 Yafe da waɗannan zan tsaya.

[V2]
 KORUS
 Kan Yesu, Fan Ceto, na tsaya,
 Ba wani wurin rai, ko ɗaya.
 Ba wani wurin rai, ko ɗaya.

[V3]
 2) Ko zunubaina sun yi yawa
 Har ba mai iya ƙirgawa,
 Ba wanda ba a shafe ba
 Ran da ka ba da jininka.
 Korus

[V4]
 3) Dabarun duniya suna nan,
 Dabarun banza na Shaiɗan.
 Tawa dabara ɗaya ce,
 Cetona jinin Yesu ne.
 Korus

[V5]
 4) Domin shari'ar Lahira,
 Yesu, na fake wurinka.
 Ban duba nawa aiki ba,
 Gare ka ne na dogara.
 Korus

[V6]
 5) A ƙofar Sama, izinina
 Sai jininka da giciyenka.
 Ko gaban kursiyi, murnata
 Jinin Yesu da ƙaunarsa.
 Korus</lyrics>
<title>Ya Yesu, Kayan Adona Jininka Ne LW184</title>
<hymn_number>184</hymn_number>
</song>